James 5

Gargaɗi ga Masu Arziki Masu Danniya

1Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. 2Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. 3Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa zata zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. 4Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin maʼaikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. 5Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka. 6Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba.

Haƙuri Cikin Wahala

7Saboda haka ʼyanʼuwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa. 9ʼYanʼuwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa! 10ʼYanʼuwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. 11Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji ɗaurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.

12ʼYanʼuwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yǎ zama “I”, “Aʼa” naku kuma yǎ zama “Aʼa”, don kada a hukunta ku.

Adduʼar Bangaskiya

13Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yǎ yi adduʼa. Akwai wani mai murna? Sai yǎ rera waƙoƙin yabo. 14Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yǎ kira dattawan ikkilisiya su yi masa adduʼa, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. 15Adduʼar da aka yi cikin bangaskiya, za ta warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. 16Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi adduʼa saboda juna, domin ku sami warkarwa. Adduʼar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

17Eliya mutum ne kamarmu. Ya yi adduʼa da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. 18Ya sāke yin adduʼa, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

19ʼYanʼuwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi, 20sai yǎ tuna da wannan: Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yǎ kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

Copyright information for HauSRK